Kotun Kolin Amurka Na Shirin Sauraren Kara Kan "Obamacare"

Ginin Kotun Kolin Amurka

Ana shirin ci gaba da sauraren kara kan tsarin kiwon lafiya mai rahusa da 'yan Republican suke adawa da shi a Kotun Kolin Amurka.

A yau Talata, kotun Kolin Amurka ke shirin fara sauraren bahasin baka a yunkurin da ‘yan Republican ke yi na ganin an soke dokar da ta samar da tsarin kiwon lafiyar nan mai rahusa ta Affordabale Care Act.

Sauraren karar na zuwa ne, makonnin bayan da Mai Shari’a Amy Coney Barret ta kama aiki a kotun, lamarin da ya ba masu ra’ayin mazan jiya rinjayen kujeru 6 yayin da masu sassaucin ra’ayi ke da uku a kotun kolin.

Wani batu da aka fi mayar da hankali a kansa a wannan kara shi ne, ka’idar da dokar ta 2010 ta gindaya, na sai mutum ya yi rijistar inshorar lafiya ko kuma a ci tarar sa.

Wasu jihohin Amurka wadanda ke samun jagorancin Texas ne suka dauki ragamar ganin an soke wannan doka da ta samar da wannan tsarin kiwon lafiya, wanda ake wa lakabi da Obamacare.