Kotun koli ta yi watsi da karar jam’iyyar APM a bisa bukatar jam’iyyar tare da jingine karar da Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP da Labour suka shigar kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu a zaben watan Febrairun don yin nazari kafin ta yi zaman zartar da hukunci nan gaba.
Kotun kolin ta kuma saurari muhawara daga lauyoyi zuwa ga jam’iyyu kan bukatar da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar na kawo sabbin shaidu kan takardun da ake zargin na jabu ne da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar wa hukumar INEC a yayin mika takardun neman takara.
Lauyan Atiku Abubakar, Mista Chris Uche, ya bukaci kotun da ta amince da bukatarsu kuma ta ba da damar daukaka kara, ta amince da dukkan bukatun da suke nema, sannan ta soke takarar shugaba Tinubu.
Tuni dai 'yan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu a game da abin da suke sa ran zai wakana a kotun koli inda mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Mal. Muhammad Baloni ya bayyana cewa, duk abin da ya kasance a kotun koli, Najeriya ita ce kasarsu kuma yana fatan gwamnatin dake kań mulki za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da tsaro, abinci, da saura ababen more rayuwa.
Dakta Yunusa Tanko, jigo ne a jam’iyyar Labour, daya daga cikin jam’iyyu uku da suka daukaka kara a gaban kotun koli kuma ya bayyana cewa ya ji dadin yadda kotun koli ta karbi bayanan da jam’iyyarsa ta gabatar.
Ko mene ne jingine zaman sauraron karar da Atiku Abubakar, jam’iyyun PDP da Labour suka shigar ke nufi, babban lauya mai mukamin SAN, Magaji Garba ya ce, kotu ta saurari jawaban dukkan bangarorin da abin ya shafa, za ta yi nazari don zartar da hukunci nan gaba.
Idan Ana iya tunawa, a ranar 6 ga watan Satumbar shekarar 2023 ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu a zaben watan Fabrairun da hukuncin da ta zartar kuma jam’iyyun da ba su gamsu da abin da ya wakana ba suka daukaka kara a kotun kolin Najeriya.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5