Lauyan Atiku Abubakar a zaben shugaban kasar da aka yi a bana, Kalu Kalu, ya ce takardun shaidar karatun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mikawa INEC na boge ne.
Yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Kalu ya ce takardun da Jami'ar Jihar Chicago ta ba su sun nun cewa takardun karatun na Tinubu ba sahihai ba ne.
Hakan a cewarsa, ya tabbatar da ikirarin da suka yi na cewa takardun na boge da gaske ne. Ita dai Fadar shugaban kasa ta musanta wannan zargi.
Lauyan ya karanta bayanan da jami'ar Chicago ta turo ya nuna dukkan takardun da Tinubu ya mikawa hukumar zabe don tsayawa takara na jabu ne.
Kazalika hatta takardar gama kwaleji da ya mika don shiga jami'ar ma na jabu ne don ta na dauke da sunan mace.
Wani bayanin kuma ya nuna Tinubu ya gama kwalejin Lagos a 1970 alhali makarantar ma an kafa ta a 1974.
Kalu ya ce takardar yi wa kasa hidima ta Tinubu na nuna Bola A. Tinubu, “A “ din na nufin Adekunle ne ba Ahmed ba.
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Mainsara Kogo Umar ya ce dama irin wannan shari'a ta na dauke da abubuwa da dama da a ka gabatar gaban kotu don kare ikirarin murdiya ko akasin haka a zaben.
Gabanin Kalu y yi jawabinsa, Atiku ya ce hakan wata nasara ce ta dimokradiyya.
"Ina so na godewa lauyoyi a nan Najeriya da Amurka da su ka taimaka wajen samun da gamsassun amsoshi ga lamarin da ya gagari hukumomin na nan gida warwarewa tsawon shekaru aru-aru." Inji Abubakar Abubakar wanda ke nuna tamkar rashin bincike ko matakai sun sa ba a gano hakikanin shiadar kammala karatun na shugaba Tinubu ba.
Kazalika Atiku ya ce yanzu ne marigayi Gani Fawehemmi zai kwanta ya huta a makwancinsa don cika ma sa burin sa na binciko irin wannan gaskiya.
Hakanan Atiku wanda dama ya ke zargin Tinubu ya mika shaidar kammala karatu ta jabu, ya ce ai duk zurawa da gudun da karya ta yi wataran gaskiya za ta cimma ta.
Dama mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul’ziz Abdul’aziz ya ce ba ya ganin Atiku da sauran wadanda su ka daukaka kra za su samu nasara a kotun koli don yanda kotun zabe ta kori hujjojin da su k ace sun gabatar.
Yanzu dai za a jira a ga yanda kotun koli za ta saurari wannan kara da kuma hukuncin da za ta zartar.
A tarihin siyasar Najeriya kotun koli ba ta taba sauke shugaban kasa ba amma ta sauke gwamnonin wasu jihohin.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna