Kotun Kolin Najeriya ta kebe ranar Litinin 23 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta fara sauraren karar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 Atiku Abubakar ya daukaka.
Atiku ya daukaka kara a kotun inda yake kalublantar nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben da aka yi a watan Fabrairun 2023.
Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ya yi takara karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, zai nemi kotun ta ba shi dama ya gabatar da sabbin hujjojin da ke neman a soke nasarar ta Tinubu na jam’iyyar APC.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labor, Peter Obi da na jam'yyar APM, Chichi Ojei na cikin wannan kara da aka daukaka.
A farkon watan Satumbar da ya gabata, kotun da ta saurari kararrakin zaben shugaban kasa ta jaddada nasarar Tinubu tare da yin watsi da korafe-korafe da Atiku da Peter na Obi na jam’iyyar Labor suka gabatar.
Kotun karkashin jagorancin Alkali Haruna Tsammani ta ce jam’iyyun PDP, LP da APM, sun gaza gabatar da hujjoji da za su nuna cewa Tinubu bai lashe zaben ba.
Wannan hukunci ya sa Atiku, Obi da Ojei suka garzaya kotun koli don ci gaba da neman a soke nasarar ta Tinubu.
A wannan karon, rahotanni na nuni da cewa Atiku zai nemi kotun ta ba shi dama ya gabatar da sabbin hujjoji.
Kamar yadda bayanai suka nuna, ana tunanin Atiku zai kalubalanci takardun karatun Tinubu da ya yi a Jami’ar Chicago da ke Amurka.
A cewar lauyoyin Atiku, takardun karatun da Tinubu ya gabatarwa hukumar zabe ta INEC na boge.
Fadar shugban kasa ta musanta zargin tare da yin watsi da shi.
A ranar Laraba Kotun Kolin ta kafa wani kwamiti mai Alkalai bakwai da zai saurari wannan kara.