ICC Ta Yankewa Jean-Pierre Bemba Hukuncin Daurin Shekaru 18 A Gidan Yari

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ta yankewa tsohon mataimakin shugaban kasar Congo, Jean- Pierre Bemba hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 18, bayan da ta same shi da laifin ingiza gudanar da ayyukan fyade da kisa a Jamhuriyar tsakiyar Afrika da ke makwabtaka da su.

Alkalin kotun Sylvia Steiner da ta fito daga Brazil, ta ce Bemba ya nuna gazawa wajen lura da ayyukan dakarunsa na kansa a shekarun 2002 da 2003, wadanda suka rika yiwa mata fyade tare da kashe mutane da azabtar da wasu.

A watan Maris, Bemba ya zamanto mutum na farko da kotun ta yankewa hukunci bayan da aka same shi da aikata laifukan yaki.

Kuma wannan shi ne karon farko da kotun ta ICC ta yanke hukunci akan fyade a matsayin laifin yaki da kuma laifukan cin zarafin bil adama.

A baya kotunan kasa da kasa irin na Rwanda da wadda aka kafa a tsohuwar Yugoslavia sun taba yanke irin wannan hukunci.

Har ila Bemba, ya zamanto mutum na farko da aka dorawa laifukan da mutanen da ke karkashinsa suka aikata.