Duk da kwanciyar hankalin da aka samu bayan tashin hankalin da akayi a farkon makon nan, har yanzu dai ana zaman ‘dar ‘dar kan iyakar kasar Habasha da makwabciyarta Eritrea.
A jiya Alhamis ne kasar Eritrea tace ta kashe sojojin Habasha sama da 200, ta kuma raunata sama da 300. Sai dai sanarwar ta ma’aikatar yada labarai bata fadi ko dakarun Eritrea nawa aka kashe ko raunata ba.
Kuma har yanzu dai babu wanda ya tabbatar da gaskiyar yawan sojon da Eritrea tace ta kashe, a sanarwar da ta fitar jiya Alhamis.
A wata hira da Muryar Amurka tayi da ministan yada labarai na Habasha, Getachew Reda, ya nuna cewa yawan sojojin da suka ce sun kashe kididdigar ba gaskiya bace, amma kuma bai musanta labarin ba.
Haka kuma yace Habasha bata da Muradin fitar da bayanan abinda ya faru a lokacin yakin.