Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa tsohon shugaban kasa Mohammed Morsi hukuncin kisa saboda baraka da aka samu a gidan kaso, wadda tayi sanadiyar guduwar dumbin ‘yan gidan yari a shekarar 2011.
Da farko dai an yake mashi hukuncin ne a watan da ya gabata tare da wasu mutane su dari.
Har wala yau kotun ta yanke ma Mr. Morsi hukuncin daurin rai yau Talata a wani batu na daban wanda ya kunshi zargin hada kai da kungiyoyin kasashen ketare, ciki har da kungiyar ‘yan bindigan Falasdinu dake Hamas.
Tun bayan bambarar da gwamnatinsa da shugaban rundunar sojan kasar a lokacin ya jagoranta, wato shugaban kasa a yanzu, Abdel Fattah el-Sissi, gwmanatin Masar ta gabatar da kare-kare akan Mr. Morsi da shugabannan kungiyarsa ta ‘Yan’uwa Musulim ko Muslim Brotherhood da aka haramta a cikin tsarin wata doka da aka yi game da kungiyar.
Hukuncin da aka yanke a yau Talata ya hada da hukuncin kisa ga shugaban na kungiyar ta Muslim Brotherhood da kuma hukuncin daurin rai ga wasu shugabannan.
Amma dai za’a iya daukaka kara don neman sassauci.