Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan Ya Sulale Daga Afirka Ta Kudu


Shugaban Sudan Umar Al-Bashir
Shugaban Sudan Umar Al-Bashir

Shugaban kasar Sudan Umar Al-Bashir ya bar kasar Afirka ta Kudu duk da barazanar kamashi da kotun laifuka ta kasa da kasa ta yi.

Yayin da yake halartar taron kungiyar kasashen Afirka a Afirka ta Kudu kotun laifuka ta kasa da kasa ta bukaci a mika Shugaba Al-Bashir ga ita akan zargin da kotun ta yi masa na cin zarafin dan Adam.

Akan haka ne wata kotu a Afirka ta Kudu ta shirya zaman jin karar yau Litinin ta yanke shawarar ko ta cafkeshi ko kuma ta bari ya tafi. Amma ta bada umurnin kada ya bar kasar har sai ta yanke hukunci.

Amma da misalin karfe goma na safiyar yau agogon Afirka ta Kudu shugaba Umar al-Bashir ya fice daga kasar daga filin jirgin sama da shugabannin kasashen waje ke yin anfani dashi.

Har lokacin da shugaban ya bar kasar kotun bata ma gama zamanta ba. To saidai duk shugabannin da suka halarci taron suna da kariya ta diflomasiya saboda haka da wuya a tsare shugaban. Banda haka shugabannin Afirka sun yanke shawarar kada su sake amincewa da kotun wurin kama wani shugaban Afirka saboda zargin cewa kotun shugabannin Afirka ne kadai take kamawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:20:43 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG