YAMAI, NIJAR - A karshe kotun ta ayyana ranar 10 ga wata a matsayin ranar za ta bayyana hukuncin da za ta yanke.
Kotun ta Cour d’Etat mai mambobi kimanin 22, a zaman da ta yi a karkashin shugabancin Mai Shara’a Abdou Dangaladima a wannan juma’a 5 ga watan Afrilu ta maida hankali ne kan bukatar da Ofishin Ministan Shari’a ya gabatar a madadin gwamnatin Nijar saboda ganin ta cire wa Mohamed Bazoum rigar kariya a matsayin matakin share fagen shirye-shiryen gurfanar da shi gaban kuliya sanadiyar zargin cin amanar kasa.
Kusa a kungiyar fafutika ta ROTAB Mahamadou tchiroma Aissami na cewa bai ga matsala ba tattare da wannan mataki.
Lauyoyin hambararren shugaban kasar wadanda Me Moussa Coulibaly ya wakilta a wannan zama, sun bukaci kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokacin na gaba ta yadda za su sami damar binciken takardun shari’ar, su kuma gana da mutumin da suke karewa.
Sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba domin alkalan kotun sun ayyana ranar 10 ga watan Afrilun dake tafe a matsayin ranar da za ta sanar da hukuncin da za ta yanke.
Magoya bayan Shugaba Bazoum irinsu Sahanine Mahamadou da ke ganin rashin cancantar hanyoyin da aka bi a yunkurin gurfanar da hambararren shugaban kasar ta Nijar na fatan ganin za a yi adalci a wannan harka.
Sakin Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa da ma mukarraban gwamnatinsa na daga cikin sharudan da kungiyoyin kasa da kasa da manyan kasashen duniya suka gindaya wa hukumomin mulkin sojan Nijar kafin su sake mayar da cikakkiyar hulda da wannan kasa yayinda mahukuntan kasar ke cewa abin na da kamar wuya saboda girman laifin da suke zarginsa da aikatawa.
A baya kotun CEDEAO ta umurci a sallame shi sai dai abin bai yi tasiri ba dalili kenan tun daga wancan lokaci kawo yau magoya bayan Shugaba Bazoum ke fassara matakin ci gaba da tsare shi a matsayin bita da kullin siyasa.
A saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5