AGADEZ, NIGER - Gwamnatin Nijar dai ta bukaci jakadan kasar Aljeriya da ya yi magana da gwamnatin kasarsa domin kawo karshen cin zarafin da ‘yan Nijar ke fuskanta da ma na wasu kasashen Afirka ta yamma.
Abdourahamane Dikko masanin harkokin yau da kullun a Nijar ya bayyana gamsuwa kan matakin na mahukuntan Nijar.
Kusan kowane karshen wata kasar Aljeriya na koro ‘yan kasar Nijar dama na wasu kasashen Afirka a cikin mawuyacin hali bayan rabasu da dukiyoyinsu kamar yadda wasu ‘yan kasar ta Nijar da kasar Aljeriya ta koro a makon da ya gabata suka shaidawa Muryar Amurka.
Acewar Sulaimane Issaka, wanda jami’in gwamnati ne, ya bayyana irin halin da mahukuntan kasar Aljeriya ke kwaso ‘yan ci ranin kasar Nijar a cikin yanayi na cin zarafi.
Masana na ganin matakin gayyatar jakadan Aljeriya a Nijar bazai kawo karshen wannan matsalar ba illa kawai hukumomin su samar da hanyoyin rage talauci a tsakanin al’umma da kuma samarda ayyuka na dai dai da sauran kasashen.
Al’ummar Nijar dai sun zura ido su ga tasirin da wannan matakin zai yi na gayyatar jakadan kasar Aljeriya a Nijar wajen shawo kan wannan matsalar ta ‘yan ci ranin Nijar a kasar Aljeriya.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna