Kotu ta Mayarda Mustapha Jakolo Sarkin Gwandu

gavel

Bayan shekaru tara da gwamnatin Kebbi ta tsige Mustapha Jakolo daga sarautar sarkin Gwandu, yanzu kotu ta mayarda shi.

Bayan ta tsige Mustapha Jakolo gwamnatin ta Kebbi a karkashin Adamu Aliero ta nada Muhammadu Iliyasu Bashar a mukamin sarkin Gwandun.

Alhaji Jakolo ya gurfanar da gwamnatin ta Kebbi a gaban kotun tarayya inda ya kalubali tsigewar da aka yi masa. A zamanta na jiya tace an cire sarkin ba bisa kaida ba. Sabili da haka ta umurci gwamnatin jihar da ta maidashi akan mukaminsa.

Barrister Ahmadu Tumaru daya daga cikin lauyoyin Mustapha Jakolo ya bayyana inda gwamnati ta kaucewa kundun tsarin mulki lamarin da yasa kotu ta mayarda sarkin kan mukaminsa. Tun can farko masu nada sarkin Gwandu sun fadawa gwamnan jihar na lokacin Adamu Aliero kada ya cireshi.

Yanzu kotu ta ruguje nadiin da aka yiwa Alhaji Bashar. Ta umurci gwamnati ta mayar dashi akan mukaminsa. Ban da haka kotun tace duk kudinsa da yakamata a bashi cikin shekaru taran a biyashi. Duk wani hakinsa tun daga lokacin da aka tsigeshi a bashi.

Sakataren gwamnatin Kebbi Garba Rabiu Kamba yace gwamnatin jihar na jiran lauyoyinta domin su gabatar mata da hukuncin. Daga nan gwamnati zata san mataki na gaba. Tana yiwuwa gwamnatin ta daukaka kara.

Mustapha Jakolo yana da magoya baya da yawa a Gwandu. Mutane sun fito suna tayashi murna cikin lumana.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Mayarda Mustapha Jakolo Sarkin Gwandu - 2' 59"