Babbar kotun tarayyar ta yanke hukumcin ne bayan sauraron karar da kungiyar NBA ta shigar a kan Pauline Tallen.
Kungiyar lauyoyin Najeriya ta maka tsohuwar Ministar a kotu saboda ta soki hukuncin da kotu ta yi a baya.
A wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta yi tir da kalaman da tsohuwar ministar ta yi a shekarar da ta wuce, inda ta caccaki wani hukuncin kotun tarayya da ke Jihar Adamawa.
Kotun da ke zamanta a birnin Yola, babban birnin Adamawa, ta soke cancantar takarar A'ishatu Dahiru da aka fi sani da Binani ta jam'iyyar APC da ke neman kujerar gwamnan a wancan lokacin.
Sai dai Tallen ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin na kotun wanda ta bayyana a matsayin "musguna wa wani bangare na al'umma", yayin da ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da hukuncin.
Kotun ta ce kalaman Tallen sun saba doka, kuma akwai ganganci da takaici da kuma rashin yi wa bakinta linzami.
Saboda haka Alkali ya zartar da hukunci cewa dole ta nemi afuwa, ko kuwa ba za ta sake iya rike mukami ba.
Sai dai tsohuwar Ministar ta nuna halin ko-in-kula, lamarin da ya sa kungiyar lauyoyin ta maka ta a gaban kotu.
Duk yunkurin jin ta bakin Pauline kan hukumcin kotun ya ci tura.