Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Wasu Masu Karfin Fada-A-Ji Da Ke Abuja Na Yi Takara, Ba Da Binani Ba – Fintiri


Gwamnan Adamawa, Fintiri (Facebook/Gwamnatin Adamawa)
Gwamnan Adamawa, Fintiri (Facebook/Gwamnatin Adamawa)

Sai dai gwamnan na Adamawa bai kama sunan wadanda yake ikirarin da su ya yi takarar ba.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP, ya ce takarar da ya yi da wasu mutane ne masu karfin fada-a-ji da ke Abuja, ba da Aishtu Binani ba.

A ranar Talata hukumar zabe ta INEC ta ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Adamwa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

“Ba da wata mata (Binani) na yi takara ba, ko APC, na yi takara ne da daukacin tsarin da madafun iko ke kai – wadanda suke Abuja, suke tunanin su suka mallaki Najeriya.” Fintiri ya fada a shirin Politics Today na tashar gidan talbijin na Channels.

Sai dai gwamnan na Adamawa bai kama sunan wadanda yake ikirarin da su ya yi takara ba.

Fintiri ya samu kuri’u 430, 861 a zaben da aka sake a jihar a ranar Asabar din da ta gabata yayin da Aishatu Binani ta APC ta samu kuri’u 396, 788.

An yi ta kai ruwa rana yayin tattara sakamakon zaben, lamarin da ya haifar da rudani a lokacin da aka ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zabe, ko da yake INEC ta soke wannan matsaya.

A ranar 29 ga watan Mayu za a sake rantsar da Fintiri a wa’adin mulki na biyu.

XS
SM
MD
LG