Kotu Ta Dakatatar Da Dawo Da Sanusi Lamido

Sanusi Lamido Sanusi II

Mai shari’a Mohammed Liman ne ya mika wannan umarnin ga gwamnatin ta Kano.

A yau ne Malam Muhammadu Sanusi II ya isa gidan gwamnatin Kano domin karbar takardar kama aiki a hukumance a matsayin sabon sarkin masarautar Kano daya tilo duk da cewa babbar kotun tarayya da ke Kano ta haramta yin hakan, bayan da guda daga cikin masu rike da mukami a masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi sarkin dawaki babba na fadar masarautar Kano ya shigar gaban kotun.

Mai shari’a Mohammed Liman ne ya mika wannan umarnin ga gwamnatin ta Kano.

Ku Duba Wannan Ma Masarautar Kano: Muhammadu Sanusi II Ya Karbi Takardar Nadinsa
Ku Duba Wannan Ma Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Da Muhammadu Sanusi Kan Mukamin Sarkin Kano

Sai dai kuma Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya ce alkalin da ya yanke hukuncin dakatar da mayar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano yana kasar Amurka.

A cewarsa, Alkalin da ba ya kasar nan ba shi da hurumin dakatar da abin da majalisar dokokin jihar ta yi ta hanyar da ta dace.