Babbar kotun tarayya dake birnin Abuja ta mika ajiyar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a hannun hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (efcc).
Kotu ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Disamba mai kamawa domin yin hukunci akan bukatar neman belin da tsohon gwamnan jihar Kogin, Yahaya Bello, da wasu mutum 2 suka gabatar mata.
EFCC ta shigar tuhumar zargin aikata almundahanar Naira biliyan 110 a kan tsohon gwamnan.
Bello yaki ya amsa tuhume-tuhume 16 da hukumar EFCC mai yaki da almundahana ke yi masa.
Tsohon gwamnan tare da Umar Oricha da Abdulsalam Hudu sun gurfana a gaban kotu a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa na 3, domin fuskantar tuhume-tuhume 16 da hukumar EFCC ke yi musu a kan badakalar naira biliyan 110.
Sun ki amsa laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa.
Bayan da aka ji ta bakin wadanda ake karar, lauyansu, Joseph Daudu, ya gabatar da bukatar neman beli. Sai dai lauyan EFCC, Kemi Pinhero, ta kalubalanci bukatar, inda tace damar yin hakan ta kare tun a watan Oktoba.
Da yake karin haske, lauyan wadanda ake kara, yace bukata daya tilo dake gaban kotun ita ce ta neman belin wanda ake kara na 1, wacce aka shigar a ranar 22 ga watan Nuwambar da muke ciki.