Kotu Ta Amince Daliban Legas Su Saka Hijabi

Wasu yara 'yan mata sanye da lullubi a lokacin sallar Eid

Bayan kwashe wani lokacin mai tsawo ana takaddama dangane da batun sanya hijabi a makarantun jihar Legas, wata kotu ta yanke hukuncin cewa dalibai mata musulmi za su iya saka hijabi a makarantun.

Alkalai biyarne suka yanke hukuncin a wata kotun kolin jihar a karkashin jagorancin A.B Gumel.

Ba a Najeriya kadai wannan batu ya janyo takaddama ba, kasashe irinsu Faransa ma sun sha fama da wannan batu.

Ita dai kotun kolin ta bayyana cewa, haramtawa mata dalibai sanya hijabi da gwamnatin ta yi a baya, ya sabawa ‘yan cin daliban na yin biyayya ga koyarwar addininsu.

Domin jin cikakken rahoto kan wannan lamari, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Babangida Jibril daga Legas:

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu Ta Amince Daliban Legas Su Saka Hijabi - 1'44"