Majalisar ta gayyaci ministanne domin yin bayanin da ake ciki wajan aiwatar da kasafin kudin bana domin tabbatar da cewa komi na tafiya bisa ka’ida kamar yadda ya kamata. Shugaban kwamitin kasafin kudi Sanata Dan’juma Goje ya ce sun gamsu da bayanan ministan musamman ganin yadda gwamnatin tarayya ke biyan albashi ba kamar yadda wasu jihohi ke samun tangarda ba.
Sanata Goje ya bayyana cewa sun gamsu da bayanan ministan domin kuwa a cewar sa gwamnatin tarayya ta taka rawar gani domin kuwa tana biyan albashi akan lokaci ba kamar wasu jihohin kasar ba. A bangaren kudaden tafiyar da ayyukan gwamnati kuma, nan ma sun yi rawar gani, domin sun bada kudi dai dai yadda aka a kasafin kudi.
Ya kara da cewa abu na uku wanda ya bada wahala shine kudin da za’a yi manyan ayyuka dasu, ko suma akwai dalilai masu karfi saboda sababbin ayyuka ne kuma ba’a fara su ba domin sai an tallatasu sa’annan abi wasu hanyoyi kafin a bada kwangila, kuma ya bayyana cewa ana kan rubuce rubuce akan lamarin.
Sai dai a bangaren sakataren gwamnatin tarayyar, majalisa ta nuna damuwa akan kalaman da ya ambata na cewar baza’a sami wadatattun kudaden gudanar da ayyukan mazabu da na ‘yan majalisar ke gudanarwa ba.
Ta dalilin haka ne sanata Yusuf Abubakar Yusuf yayi Karin bayanin cewa tunda ayyukan mazabu basu kai kashi guda cikin dari ba a cikin kasafin kudin kasar, yana ganin wajijbi ne a gudanar da ayyukan domin a cewar sa idan sun koma mazabunsu su nanata wa jama’a irin ayyukan da suka yiwa al’umomin su bisa alkawarin da suka dauka.
Ga rahoton Madina Dauda.