Kwamitin binciken y ace, dole a hukunta wannan babban kwamanda da kuma wasu hafsoshin bisa laifin wuce gona da iri da suka yi wajan fuskantar wannan lamari.
A mayar da martani daga jami’an sojin, Kakakin shalkwatar sojin Najeriya kanar Sani Usman Kuka Sheka, ya ce zuwa yanzu, babu abin da rundunar sojin kasar zata ce har sai lokacin da gwamnatin jihar ta Kaduna ta fitar da takarda akan wannan rahoto.
Kanar Aminu Isa Kwantagora, tsohon gwamna a lokacin mulkin soja a jihohin Kano da Benue yace a duk lokacin da babban kwamandan soji yakai mutanensa wani wuri, kuma ta kasance ana barazanar yi masu rauni, ko hallaka su, dokar soja ta bashi umurni ya kare sojojin sa, domin bazai iya fadawa soja cewa an hallaka ko jima sojojinsa rauni saboda bai sami izini ya dauki wani mataki ba.
A bangaren masu shari’a kuma, barista Yakubu S. Bawa Malumfashi kwararren lauya ne a Najeriya yace a shari’ance duk wanda ake zargi da aikata laifi, a bada shaidar laifin da ya aikata, dan haka ya kara da cewa shin kwamitin da alhakin ya rataya a wuyansa ya kira wanda ake zargi domin yi masa tambayoyi?.
Muhammed Ibn’ Ibrahim, editan jaridar ‘yan shi’a mai suna Ahlal Baiti, ya bayyana cewa kawo yanzu dai wani bangaren rahoton ne kadai ya kai garesu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina Daga Abuja.