A wajan taron tallafawa wadanda ‘yan Boko haran suka yi sanadiyyar rasa hanu ko kafa da sauran masu irin wannan larura ta dalilai daban daban, malaman kungiyar Ismala ta JIBWIS sun ce ya zama wajibi malamai su dage wajan cusa sahihiyar akida irin ta Islama dake koyar da zaman lafiya, da talafawa marayu, da ‘yan gudun hijira, da matan da suka rasa mazan su, da sauransu.
Dr Alhasan Sa’idu Adam Jos, ya ce duk wanda ya kashr rai batare da hakkin shari’a ba da sunan musulunci ayi watsi da ikirarinsa a duba tanadijin da yake cikin Alkur’ani mai girma.
Shugaban JIBWIS Sheik Abdullahi Bala Lau, ya ce nasarar murkushe ‘yan ta’adda ko rage kaifin tasirinsu a Najeriya kadai ya isa abin kwanciyar hankali ko da kuwa ana cikin kuncin rayuwa da talauci a kasar.
Mahalarta taron sun tafi da nufin isar da muhimmancin taimakawa juna domin hakan zai kawo saukin al’amurra a Najeriya.
Daga karshe a lokacin rufe taron, anga jami’an kera hannu da kafafun roba daga kasar indiya na gwada wani karamin yaro da ya rasa kafafunsa biyu sakamakon kuskuren yi masa allura a asibiti, sai kuma wata mata data rasa kafarta tun zamanin mulkin soja na marigayi Murtala a shekarar 1976.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.