Wata kotu a Koriya ta Kudu ta ba da sammacin kama tsigagge kuma dakataccen shugaban kasa Yoon Suk Yeol akan kwarya0kwaryan yunkurin da yayi na kakaba dokar soji, kamar yadda masu bincike suka bayyana a yau Talata.
Shugaba Yoon ya dakatar da mulkin farar hula na dan wani lokaci a ranar 3 ga watan Disamban da muke ban kwana da shi, inda ya jefa kasar cikin mafi munin rikicin siyasar data jima bata ga irinsa ba.
Majalisar Dokokin kasar ta kwace ikonsa na shugaban kasa sakamakon al’amarin, saidai ana jiran hukuncin kotun tsarin mulkin kasar akan ko za’a tabbatar da tsigewar.
“An bada sammacin kame dana bincike a yau da safe,” kamar yadda sanarwar da shelkwatar binciken kasar ta fitar ta bayyana.
Shugban mai ra’ayin rikau na fuskantar tuhume-tuhume akan tunzura al’umma, wadanda ka iya janyo masa daurin rai da rai koma hukuncin kisa baki daya.
Jami’an dake gudanar da bincike a kan ayyana dokar sojin da Shugaba Yoon ya yi ne suka bukaci sammacin a jiya Litinin bayan da ya ki bayyana domin amsa tambayoyi a karo na 3.