Koriya Ta Arewa Ta Yi Gwajin Harba Makamai Daga Ruwa Zuwa Tudu

This picture taken on January 25, 2025 and released from North Korea's official Korean Central News Agency (KCNA) via KNS on January 26, 2025 shows the test-firing of a sea-based (underwater) ground-to-ground strategic cruise guided weapon, at an undisclo

Gwajin makaman da Pyongyang ta yi shi ne na farko tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadar White House a ranar Litinin.

Koriya ta Arewa ta yi gwajin harba makamai masu linzami na jirgin ruwa zuwa tudu, a cewar kamfanin dillancin labarai na KCNA a yau Lahadi, inda ya kara da cewa makaman sun dira a daidai inda aka auna su.

“Ana kara kyautata hanyoyin dakile yaki na sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Korea," in ji shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, yayin da yake sa ido kan gwajin da aka yi a jiya Assabar, in ji kamfanin dillancin labaran.

Makaman sun dira kan inda aka auna su bayan da suka yi tafiya mai tsawon kilomita 1,500 a cewar rahoton, inda ya kara da cewa "ba’a sami wani mummunan tasiri ba ga tsaron kasashe makwabta."

KCNA ba ta bayyana inda aka yi gwajin ba.

Gwajin makaman da Pyongyang ta yi shi ne na farko tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadar White House a ranar Litinin.

Jim kadan kafin rantsar da shi, Koriya ta Arewa ta harba makamai masu cin gajeren zango a cikin teku.

Trump, wanda yayi jerin ganawa da ba sabam ba da Kim a wa'adin mulkinsa na farko, ya fada a wata hira da aka watsa a ranar Alhamis cewa, zai sake ganawa da Kim, yana mai kiran shugaban na Koriya ta Arewa a matsayin "mutum mai wayo."

Kasashen Koriya biyu sun ci gaba da zaman doya da man ja tun karshen rikici tsakaninsu daga shekarar 1950 zuwa 1953, wanda ya kare da makamai, ba yarjejeniyar zaman lafiya ba.

Dangantaka tsakanin Pyongyang da Seoul tana daya daga cikin lokaci mafi muni a cikin shekaru, inda Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami a bara wanda ya saba wa takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata.