Kocin Dortmund Ya Yi wa Halaand Fatan Alheri

Mai horar da 'yan wasan Dortmun Marco, hagu da Halaand a dama

A watan Maris Barcelona ta nuna sha’awar sayen Halaand amma matsalolin kudade da take ci gaba da fuskanta sun sa ala tilas ta janye.

Mai horar da ‘yan wasan Borussia Dortmund Marco Rose, ya yi wa Erling Halaand fatan alheri bayan da Manchester City ta saye shi.

A ranar 1 ga watan Yuli kwantiragin Halaand zai fara aiki a City wacce ke rike da kofin gasar Premier League ta Ingila.

“Muna masa fatan Alheri, domin ya ba mu gudunmowa da dama, ya zura mana kwallaye, ya kara mana kuzari. Halaand dan wasa ne da a ko da yaushe yake son ya ga ya samu nasara.” In ji Marco kamar yadda AP ya ruwaito.

Marco ya kara da cewa, Borussia Dortmun ba za ta daina buga wasa ba saboda Erling ya tafi.

Ya kara da cewa, duk da kwarewarsa “ina ga akwai wuraren da yake bukatar ya kara mayar da hankali wajen inganta wasansa.”

“Har yanzu matashi ne. Ina ganin watakila za mu sake haduwa. Ina fatan mu sake haduwa, mun hadu da shi a Salzburg a baya.” Marco ya ce.

A ranar Talata City ta bayyana sayen dan wasan, wanda ya kasance babban kamu a kasuwar cinikin ‘yan wasan kwallon kafa.

A watan Maris Barcelona ta nuna sha’awar sayen Halaand amma matsalolin kudade da take ci gaba da fuskanta sun sa ala tilas ta janye.