Koch Gerardo Ya Kare Messi Kan Suka Da ‘Yan Argentina Ke Masa

Argentina's forward and captain Lionel Messi reacts after losing the 2014 FIFA World Cup final football match between Germany and Argentina 1-0 following extra-time at the Maracana Stadium in Rio de Janeiro, Brazil, on July 13, 2014.

Lionel Messi shine dalilin muhawarar da ake tafkawa a kasar Argentina, wata guda kenan bayan da Chile ta murkushe ta a gasar Copa America, a jiya Talane ne koch Gerardo Martino yace, idan da shine Messi da ya dade da daina bugawa kasar wasa a dalilin sukar da aka dade anayi masa.

Ya ci gaba da cewa babu irin wannan muhawara a Bercelona, meyasa ba’ayi a can? Messi dai ‘dan wasa ne da ya ajiye tarihi a duniya, a baya ya sami nasarar zama zakara a wasanni dabam dabam da suka hada da Camp Nou da Liga da Copa del Rey, a kakar wasan da ta wuce ma ya sami zama zakaran Champion Lig.

Yanzu da yake ya dawo kuma zai yi farin cikin barin gardamar da ake waje, abin takaici dai shine yadda ake ci gaba da shakkar sa a kasar sa, suka kan Messi ba yana nuna ana yaba masa bane. Inji babban koch din Argentina Gerardo Martino.

Duk da yake dai ire-iren wannan suka da muhawara a kan ‘dan wasa abu ne mai ciwon gaske, musammam ma ga ‘dan wasan da ya sami rashin sa’a a wasannin da yayi na baya bayan nan, lokacin da yayi kokarin taimakawa kasar sa a gasar cin kofin duniya da akayi, san nan kuma gasar Copa America.