Tawagar ‘yan wasan kasa da shekaru 23 sun sami shiga gasar cin kofin matasan Afirka wato U-23 da za’a yi a Senegal, bayan da suka yi kunnen doki da takwaransu na kasar Congo a babban birnin kasar Pointe Noire.
Matasan Samson Siasia sun sami nasarar lashe wasan su na farko a Port Harcourt, kuma suka kare kansu a gida.
Yanzu haka dai Najeriya ta shiga jerin kasashen Afirka kamar su Algeria da Afirka ta Kudu da Zambia da Tunisia, wadanda suka sami shiga gasar da za’a yi mai hadakar kungoyoyin wasa takwas, wanda za’a fara a watan Disamba mai zuwa na wannan shekarar.
Koch Siasia ya yabawa ‘yan wasan sa inda yake cewa sunyi aikin su dai dai, duk da yake akwai lokutan da yakamata suma zarga kwallo raga amma basuyi ba. ya kara da cewa buga wasa irin wannan abune mai wahala, amma sun riga sun san dabarun wasan mu, inda suka tafi baki dayan su suna kai hari.
A Gasar dai za’a zabi kasashe uku da zasu wakilci nahiyar Afirka a wasan Olympic na shekara ta 2016 da za’ayi a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.