Batutuwan da suka shafi, baki ‘yan cirani, diyaucin kasa, da tsaro da kuma makomar tattalin arzikin Birtaniyya sune a zukatan masu kada kuri’a ta farko yau Alhamis a zaben jin ra’ayi na tarihi da kasar ke yi, wadda sakamakon a karshe zai nuna ko kasar zata cigaba da kasancewa a cikin tarayyar Turai ko a’a.
WASHINGTON, DC —
Ga wadanda suka jimrewa da ruwan sama da aka yi da safe a London, muradansu su ragu zuwa neman zaman lafiya, wadda ita ce turbar da aka kafa Tarayyar ta Turai.
Yayinda masu kada kuri’a suka isa rumfunan kada kuri’a, ra’ayoyin jama’a sun nuna cewa bangarorin biyu sun yi kunnen doki a matsayinsu kan batun.
Ana sa ran masu kada kuri’ar zasu fito da yawa, don kawo karshen watanni biyu da aka kwashe ana gudanarda kemfe mai zafi, musamman kan maganar baki 'yan cin rani, wadanda yawansu ya linka har sau biyu tun daga shekarar 2000.