Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sanatoci Sun Sake Tada Batun Mallakar Bindiga A Amurka


US Congress; Ginin Majalisar Dokokin Amurka
US Congress; Ginin Majalisar Dokokin Amurka

Kwana daya bayan da majilisar Dattijan Amurka ta dakile hanyoyi 4 da za a bi domin daukar matakin anfani da bindiga, Yanzu haka kuma wani sabon tanadi daka iya tada jijiyan wuya a majilisar ya kunno kai,biyo bayan kin daukar matakin da ake jin ya dace akan kisan da a kayi mafi muni a birnin Orlando na jihar Floroida.

Wadanda suka sake tada wannan batu kuwa sune wadanda sau tari basu faye amincewa da juna ba akan wasu manufofin gwamnati, cikin su ko harda masu ra'ayin tsaka tsaki.

Batun wanda aka tado shi jiya Talata,zai hana a sayar da bindiga ga wadanda ake tuhumar cewa ‘yan taadda ne, kuma aka hana su shiga jirgin fasinja domin inganta matakan tsaro a tashoshin jiragen saman Amurka.

Sai dai kuma wadanda aka sa sunayen su cikin wannan jerin suna da damar kalubalantar hakan tare da neman a biya su diyya wanda zai tabbatar cewa lallai kuskure ne aka yi wajen sa sunan su a jerin wadanda ake sawa ido.

Daya daga cikin wadanda suka sake tada wannan batu ko, ita ce Sanata Susan Collins tace manufar su ita ce su tabbatar Amurka ta samu dukkan kariyar da take bukata.Tace domin ba shakka harin San Bernadino dana Orlando wanda suka lakume rayuka masu yawa, yana bukatar a sake duba wannan al'amari’.

Shima Sanata Bill Nelson na jihar Florida wanda yana cikin sahun wadanda suka sake tada wannan batu, yace wajibi ne ya tabbatar wa mutanen Orlando cewa anyi wani abu akan wannan batu.

Mutane tara ne suka sa hannu akan bukatar a sake tattaunawa kan wadan nan batu 4 daga jamiyyar Republican 4 kuma daga jamiyyar Democrat sai mutun daya dan Indifanda

XS
SM
MD
LG