A cikin satin data gabata ne dai sojojin Iraqi suka sake kwato birnin Fallujah daga kungiyar ISIS, da ta rike da birnin har na tsawon shekaru biyu.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta kiyasta cewa kusan mazauna wannan birnin na Fallujah da yawan su yakai dubu 85 suka bar matsugunnin su zuwa cikin babban birnin kasar wato Bagadaza, kuma wadannan bayin ALLAH na bukatar taimako yanzu haka.
Sai dai kwamitin bada agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya aa bada dala miliyan 17 da rabi a ranar Littini domin taimakon wadannan mutanen.
Amurka tace wannan gudummawar data ce zata bayar yana daga cikin taimakon jin kai data kudiri aniyar bayar wa cikin wannan shekarar. Tace ‘yan kasar Iraqi sama da miliyan 3 aka tilasta musu zagaye cikin kasar tun a cikin shekarar 2014 domin gudun kar ayi fada.