Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Amurka 'Yan Majalisa Na Jam'iyyar Democrat Suna Zaman Dirshen Akan Bindiga


Paul Ryan kakakin majalisar wakilan Amurka dan Republican da jam'iyyarsa bata son a yi dokar binciken kwakwaf kafin a sayarwa mutum bindiga
Paul Ryan kakakin majalisar wakilan Amurka dan Republican da jam'iyyarsa bata son a yi dokar binciken kwakwaf kafin a sayarwa mutum bindiga

Anan Amurka kuma, mako na biyu kenan a jere, da 'yan jam'iyyar Democrat a majalisun dokokin Amurka suke hana ayyukan majalisa baki daya, domin neman majalisa ta dauki mataki kan tarzomar da ake yi da bindigogi matsalar d a ta addabi al'ummar kasar daban daban, na baya bayan nan shine wadda aka yi a Orlando na jihar Florida.

Jiya Laraba wakilai 'yan Democrat a majalisar wakilai, karkashin jagorancin fitattacen dan majalisa wanda ya shahara a zamanin yaki da kwatowa bakake 'yanci John Lewis daga jihar Georgia, suka fara zaman dirshen a tsakiyar zauren majalisar, har sai majalisar ta amince zata gabatar da doka kan batun saye da kuma mallakar binidga.

"A cikin shekaru 12 da suka wuce,laifuffuka da aka tafka da bindigogi, sun halaka Amurkawa fiyeda abunda cutar kanjamau ko sida ta kasha kuma fiye da wadanda suka halaka a fagen yaki, ko wadanda shaye shayen muggan kwayoyi baki daya suka kashe," inji dan majalisa John Lewis cikin wasika da ya aikewa kakakin majalisar Paul Ryan, wacce a cikinta ya bayyana cewa zasu dauki wannan mataki.

Da farko 'yan Republican suka buga kulkin kakakin majalisa da nufin neman a natsu. Amma da wakilai 'yan Democrat suka ki watsewa, 'yan Republican suka ce majalisar tana hutu na dan wani lokaci, suka kashe na'urarorin magana. Kodashike akwai hasken lantarki, an dakatar da nuna abunda yake faruwa a zauren majalisar ta talabijin, domin ana nuna abunda yake faruwa a zauren ne lokacinda majalisa take zamanta.

Nan da nan 'yan Democrat suka kaddamar da wasu hanyoyin nunawa duniya zanga zanag da zaman dirshen da suke yi.

Wakilan sun sami dauki daga takwarorinsu a majalisar dattijai wadanda suka taka suka hade da wakilan a zanga zangar da suke yi.

XS
SM
MD
LG