KWARA, NIGERIA - Amma da suka je tsakiyar ruwan sai jirgin ya fashe. Malam Sani ya ce “ya zuwa yanzu an sami gawarwakin mutane 15 kuma ana ci gaba da neman sauran har yanzu’’
A lokacin da Muryar Amurka ta tuntubi babbar jami’ar hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya - NEMA, mai Kula da jihohin Kwara da Neja, Hajiya Zainab Sa’idu ta ce ba ta riga ta samI labarin ba amma za ta tuntubi jami’anta da ke jihar ta Kwara.
Shugaban Karamar Hukumar Patigi Muhammad Ibrahim Liman ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce suna gudanar da bincike domin gano dalilin fashewar jirgin kwale-kwalen.
Idris Kpata Muhammad, sakataren karamar hukumar mulki ta Patigi ya ce lamarin ya tayar da hankalinsu matuka, amma kuma sun dauke shi a matsayin mukaddari ne daga Allah.
A baya an sha samun hadurran jiragen ruwan kwale-kwale a cikin kogunan Kwara da Neja da su ka yi sanadiyyar asarar rayuk kan jama’a, al’amarin da masu fashin baki suka ce yana bukatar daukar matakin shawo kan wannan matsala.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5