Akalla mutane 155 ne suka jikkata, yayin da barnar da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ta tilastawa mutane fiye da 80,000 barin gidajensu. Kimanin mutane 15,000 sun fake a makarantu, da wuraren motsa jiki da sauran wasu matsugunan wucin gadi.
Ambaliyar ta haddasa barna sosai, ciki har da zabtarewar kasa, da lalata tituna da kuma gadoji a fadin jihar. Jami’ai sun bayar da rahoton katsewar wutar lantarki da hanyoyin sadarwa. Mutane sama da 800,000 sun rasa hanyar samun ruwan sha, a cewar hukumar kare farar hula ta kasar, wacce ta ambaci alkaluman kamfanin samar da ruwa na Corsan.
Da yammacin ranar Asabar, mazauna garin Canoas sun sami kansu cikin ruwa mai tabo shan kai, sun yi ta gwagwarmayar kwashe mutane a cikin kwale-kwale don kai su mafaka, kamar yadda wani bidiyo da kafar yada labarai ta UOL ta yada.
Ruwan kogin Guaiba ya kai tsayin mita 5.33 da karfe 8 na safiyar Lahadi agogon kasar, yawan ruwan da ya zarta wanda aka gani a lokacin ambaliya ruwa na tarihi ta auku a shekarar 1941, lokacin da tsawon ruwan kogin ya kai mita 4.76.
"Ina nanata cewa, barnar da muka gani ba a taba ganin irinta ba a baya," a cewar Gwamnan jihar Eduardo Leite a safiyar Lahadi. A baya ya ce jihar za ta bukaci "wani gagarumin shiri” na sake farfado da ita."
Shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya je birnin Rio Grande do Sul ranar Lahadi, tare da ministan tsaron kasar José Múcio, da ministan kudi Fernando Haddad, da kuma ministar muhalli Marina Silva da dai sauransu.
A yayin gudanar da sujadar Lahadi a fadar Vatican, Fafaroma Francis ya ce yana yi wa al'ummar jihar addu'a.