Kimanin Kananan Yara 194,000 Suke Mutuwa ta Dalilin Cutar Gudawa a Najeriya

South Korean army soldiers demonstrate their martial arts skills during the 66th anniversary of Armed Forces Day at the Gyeryong military headquarters in Gyeryong.

Likitoci sun bada shawarar shayar da jarirai da nonon uwa domin kare su daga kamuwa daga cutuka da suka hada da gudawa
Directa Janar na hukumar kula da ingancin magunguna (NAFDAC), Dr. Paul Orchi ya bayyana cewa fiye da kananan yara 194,000 kasa da shekara biyar na mutuwa daga cutar gudawa.

Orchii yayi wannan bayanin a Makurdi, babban birnin jihar Benue, sa`adda yake bayani a bukin da aka shirya domin tunawa da ranar shayar da jarirai da nonon uwa na shekata ta 2013.

Yayi kira cewa wannan babbar alama ce da kuma kira ga iyaye mata a Nigeriya, su tabbatar da sun shayar da ‘ya’yansu da nonon uwa lokacin da suke jarirai zuwa a kalla shekara daya.

Orchii ya tabbatar da wannan bisa ga ruhoton asusun tallafawa kananan yara UNICEF.
Rahoton asusun UNICEF yace ya kamata a ba yara nono na tsawon shekaru biyu saboda wannan yana taimako su sami mayakan jiki dake kiyaye cututtuka, ya gargadi iyaye mata suyi kokari domin mahimmanci wannan shayarwa

Yace, kimiya ta tabbatar da cewa babu wani abun da ya kai shayad da nono wajen renon jariri,kuma, nono na dauke da magani mai kiyaye jarirai daga cututtukan yara.

Orchii ya yi Karin bayani cewa, nonon uwa bashi da wata illa, kuma kusan kowacce uwa na da isheshe da jaririnta zai bukata yakan kuma kiyaye lafiyar uwa ta wurin tsaida zubar nono da kuma maida mahaifa yadda take bayan haihuwa da kuma kiyaye kansar nono.

Cikin jawabin ta a taron, uwar gidan Gwamnan Jihar Benue, Mrs. Yemisi Suswam, , ta roki iyaye da cewa su dauki shayad da nono da muhimminci don kare lafiyar `ya`yan su, kansu da kasa duka.