Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bullar Kwayar Cuta A Saudiya


Maniyata a Makka
Maniyata a Makka

An samu bullar kwayar cuta a Saudiya da aka sama suna korona mai sarin hallaka mutum idan ba'a farga da wuri ba.

A Saudiya an samu bullowar wata kwayar cuta da aka sama suna korona. Kwayar na haddasa ciwo da ka kaiga mutuwa farat idan ba'a kula da wuri ba.

Kwayar cutar a fara samunta ne a shekara 2012 a kasar Saudiya. Ana kamuwa da ita ta hanyar tari da mura da kuma idan mutane suna shan hannu da juna.Kwayar tana haddasa tari da mura da sanyin hakarkari da ake kira nimoniya. Kwayar ana iya yadata ta hanyar cinkoson mutane.

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Najeriya da Kungiyar Kula da Kiwon Lafiya Ta Duniya sun zauna sun yi muhawara su tabbatar cewa cutar bata kawo illa ga maniyata ba da Najeriya da ma duniya gaba daya. Ta dalilin haka a saka wasu matakai a Saudiya domin dakile duk wata illa. Akwai naurori a duk filayen saukar jirgi a Saudiya da zasu binciki duk wadanda suka isa kasar a tabbatar babu wanda yake dauke da kwayar. An kuma bude asibitoci da yawa da ma'aikatan kiwon lafiya da zasu rika yawo domin koda ta kwana.

Hukumomin Najeriya sun baiwa duk wadanda ke da ciwon sukari da hawan jini da sankarau da kanjamau shawarar kada su je Saudiya bana.Amma kuma idan sun je akwai abubuwan da aka tsara su yi. Su dingi wanke hannuwansu suna kuma sa abun rufe baki da hanci. Idan kuma mutum ya fara mura da zazzabi to an umurceshi ya tuntubi jami'an Najeriya dake tare da su domin kulawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG