Jami’an kiwon lafiya a jihar dai sun yi amfani da makon wajen nuna muhimmancin taimakawa uwaye wajen samun shayar da jarirai cikin tsanaki. Ndaki Muhammad darektan kula da magunguna da abinci masu gina jiki na ma’aikatar lafiyar jihar Naija yace shayar da jariri a watanni shida na farkon haihuwarsa a duniya na da matukar muhimmanci domin haka ana bukatar taimakawa iyayen.
Haka kuma yace gwamnati tana bukatar kula da abubuwan da mace mai ciki take bukata, kamar yanayin hutu da kuma hutu bayan haihuwarta. Yace dole ne a ga cewa an basu hutu lokacin da suke bukata kada a hana su.
Wata uwa da ta halarci bukin tace akwai banbanci tsakanin yaron da ya sha nonon uwa da wanda bai sha ba. Bisa ga cewarta, yaron da ya sha nonon uwa yana da basira sosai fiye da yaron da bai sha nono ba, haka kuma iliminsu ba daya bane.
Ta kuma ce koshin lafiya na yaron da ya sha nono da wanda bai sha ba dabam yake. Tace wanda bai sha nonon uwa kullum cikin ciwo yake, amma yaron da aka bashi nono yana da wuya ya yi ciwo.
Gwamnatin jihar Naija dai tace tana fadar da mutanen a yankunan karkara game da wannan lamarin.
Wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya aiko da wannan rahoton.