Hakan ko ba zai rasa nasaba da rashin samar da kotun kasa da kasa da kasashen duniya suka yi ba, domin hukunta masu aikata wannan danyen aikin, inji wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya MDD.
Lamarin take hakkin bil’adama a wannan kasar, musammam abinda ke da nasaba da fyade, abin ya wuce hankali, kuma ba wani abu da ake yi, Inji shugaban hukumar kare hakkin bil adama ta MDD da ke kasar Sudan ta Kudu.
Yasmin Sooka ta fada wa kwamitin kare hakkin bil adama a jiya talata, a Geneva, cewa anfi gallazawa farar hula musammam ta la’akari da kabilar su kuma gwamnati ce da sauran masu alaka da gwamnatin ke wannan danyen aikin.
Ta ce yanzu haka gwamnati ta fara yekuwar sake wa wasu matsugunni ta la’akari da kabilar su, yayin da kasar ke ci gaba da kasancewa cikin yaki da kuma kisan kare dangi.
Sooka tace yanzu kame mutane, fyade, da kashe su ya zama ruwan dare a wannan kasar, Shugaban kare hakkin bil adaman ta bayyana cewa an kone kauyuka kurmus, kana an kai wa asibitoci da wuraren ibada hari.
Ta ce babban abin takaicin shine yadda aka ki hukunta masu aikata wannan danyen aikin.
Tace hanyar da kawai za a hana aukuwar wannan mummunan aikin shine ta gaggauta samar da kotun da za ta gurfanar da masu aikata wannan mummunar tabi’ar, kuma ya zamo kotun ta fara aiki a kalla zuwa karshen shekara.