Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Habasha Gocewar Laka Ta Hallaka Mutane 46


A kasar Habasha ko Ethiopia, gocewar laka a wata dalar shara ta halaka akalla mutane 46, wasu da dama kuma sun bace, a wani wuri dake wajen Addis Ababa babban birnin kasar.

Jiya Lahadi jami'an kasar suka bada labarin cewa galibin wadanda bala'in ya rutsa da su mata ne d a yara, wadanda walau kusa da wurin suke da zama, ko kuma masu tonon bola ne domin wani abu mai amfani da zasu sayar.

Shaidun gani da ido suka ce dalar sharar ta rufta cikin sauri wadanda suke kusa basu sami lokaci na gudun tsira ba.

'Yansanda kasar sun hakikance kimanin mutane dari uku ne suke da zama a inda dalar take, inda wasu daruruwa suke zuwa dalar ko wace rana domin tsintar bola.

Gwamnati ta daina kawo shara daga birnin mai mutane milyan hudu da tattalin arzikinsa yake bunkasa zuwa wannan wuri, amma daga bisani ta dawo kawo shara wurin bayan da manoma da suke kusa sabon juji suka koka yasa gwamnati ta koma amfani da wannan da ya rutsa da mutanen.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG