Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Samu Hamma Amadu Da Laifin Safarar Jarirai


NIGER: Jam'iyyar Adawar Nijar MNSD LUMANA ta Hamma Ahmadu
NIGER: Jam'iyyar Adawar Nijar MNSD LUMANA ta Hamma Ahmadu

Wata Kotu a Nijar ta samu wani madugun 'yan adawa da ke kasar waje a yanzu, da laifin safarar jarirai, ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekara guda a gidan yari.

Hamma Ahmadu, wanda shi ne babban mai kalubalantar Shugaba Mahammadou Issoufou a zaben Shugaban kasar da aka yi bara, ya na zaune ne a kasar Faransa kuma ya na can aka yanke masa hukunci.

Lauyoyin Ahmadu dai sun fice daga Kotun a Nyamai jiya Litini tun kafin ma a karanta hukuncin, su na masu cewa makasudun wannan shari'ar shi ne kawai a hana Ahmadu sake tsayawa takara. Tun da dadewa su ka tsaya kai da fata cewa zarge-zargen da ake ma Ahmadu bita-da-kullin siyasa ne kawai.

Ahmadu daya ne daga cikin wasu mutane, ciki har da matarsa, da ake zargi da safarar jarirai daga Najeriya mai makwabtaka da Nijar, inda su ke binta kasar Benin sannan su kai ma wasu attajirai a Nijar.

Wadannan zarge-zargen da aka ma Ahmadou sun fara bulla ne a 2014 lokacin da ya ke Shugaban Jamalisar Dokokin Kasar. Jim kadan sai aka kwabe masa rigar kariya ta Majalisa don haka sai ya gudu zuwa Faransa.

Wannan zargi da ake ma Ahmadu ya yi ta daukar sabbin salo; da farko wata kotun Nijar ta yi watsi da shi a 2015, sai kuma wata kotun daukaka kara ta maido da shi daga bisani a shekarar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG