A farkon shekarar nan ne gwamnati ta nemi a samar da dokar tare da ba da kwanaki 30 domin al'umar kasar su fadi ra'ayinsu dangane da dokar wanda wa'adinsa ya cika a yau Juma'a.
A wannan doka da ake son samarwa, gwamnati na so ta bar cinikayyar cikin gida kan hauren naman dajin na Mugun-dawa da kuma bari a fita da hauruka guda biyu kacal a lokaci guda ga wadanda za su amfani da shi na kashin kansu amma a karkashin wasu tsauraran dokoki.
Hukumar dake kula da muhalli a kasar ta Afrika ta kudu, ta gabatar da bukatar cewa sai an samu cikakken bayanin masu hadahdar haurukan da takardar izni da kuma nau'in hauren da aka sayar.
A shekarar 2009 aka haramta hadahadar sayar da hauren Mugun-dawa a Afrika ta kudu.
Facebook Forum