Yanzu haka rundunar 'yan sandan kasar na bincike kan wani matashi dan kasar Nijar da take tuhuma da kisan matar makwabcin sa tare da diyar ta a jihar Kebbi.
Baya ga ayukkan ‘yan bindiga da ke hana ‘yan Najeriya barci da ido biyu rufe a sassan arewacin kasar, hakama wasu miyagun mutane na ci gaba da aikata ayukkan ta'addanci yadda suka tsara.
A jihar kebbi dake arewa maso yammacin kasar wani matashi ne dan asalin Jamhuriyar Nijar ake tuhuma da kashe matar aure yar shekara 25 da diyar ta yar shekara 4, ya bar su kwance cikin jini, jaririyar ta ‘yar wata 4 ce kadai ya bari lokacin da mijin matar wanda ke Dinkin Tela yake shagon sa wurin aiki.
Faruwar wannan lamarin ya sa rundunar 'yan sanda ta dukufa ga gudanar da bincike.
SP Nafi'u Abubakar shi ne kakakin rundunar a jihar kebbi. Ya ce sunyi nasara kama wannan matashin mai shakara 25 kuma ya amsa laifin.
Luba Altine Ladan makwabciyar gidan da aka yi kisan ta bayyana wa manema labarai yadda ta ke cikin tsananin tashin hankalin.
Sahura Mukhtar yayar matar da aka kashe ita ma ta nuna kaduwa sosai a zantawar ta da manema labarai.
Yanzu dai rundunar 'yan sandan tace zata gudanar da matashin gaban kuliya, sai dai da yawa ‘yan Najeriya na ganin an sha kama masu laifi ana gurfanar da su ba'a sake jin komai.
Masanin akan aikata laifuka da tsaro detective Auwal Bala Durumin Iya, na ganin rashin kammala bincike da cikakken hujjoji ko kuma tsoma bakin ‘yan siyasa ga harkar shara'a na daga cikin abubuwan da ke sa ake ganin ba'a hukumta masu aikata manyan laifuka.
‘Yan Najeriya dai na cike da fatar ganin an samu sauyi daga abubuwan da kan ci gaba da jefa rayukan ‘yan kasa cikin halin kunci.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5