Kawar da kungiyar ISIS shi ne kan gaba - Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama

Biyo bayan hare -haren da wasu 'yan ta'ada suka kai birnin Brussels da kungiyar ISIS ta dauki alhaki shugaban Amurka Barack Obama yace kawar da kungiyar shi ne abun da ya sa gaba yanzu.

Kwana daya bayan da wasu 'yan ta'ada suka kai hari kan birnin Brussels dake Belgium da kungiyar ISIS ta dauki alhakinsa, shugaban Amurka Barack Obama yace kawar da kungiyar daga doron kasa ne abun da gwamnatinsa ta sa gaba yanzu.

Yayinda yake jawabi a kasar Argentina shugaba Obama ya lashi takobin yin duk abun da ya wajaba domin baiwa abokiyarsu kasa Belgium goyon bayan gurfanar da duk wadanda suke da hannu a hare-haren gaban shari'a su fuskanci hukumci.

Shhugaba Obama "yace wannan abun da ya faru tamkar kara mana tuni ne cewa dole duniya ta hada kai mu manta da banbancin inda muka fito da kabilanci ko kuma addininmu mu yaki ta'adanci"

Yaka kara da cewa "babbar manufata itace kakkabe kungiyar ISIL da kawar da ita da zummar kawo karshen da kisan rashin imani da take yadawa a duniya.