Gwamnatin Shugaba Donald Trump na ta fadi-tashin ganin ta nuna cewa, kudancin iyakarta da Mexico, babbar barazana ce da ka iya jefa al’umar Amurka cikin mawuyacin hali, ta kuma kawo cikas ga harkokin tsaron kasar.
Gwamnatin na kokarin yin hakan ne, domin neman a mara mata baya a kikikakan da take yi tsakaninta da ‘yan majalisar dokoki, lamarin da ya sa a yau, aka shiga yini na 18 da dakatar da ayyukan wasu ma’aikatun gwamnati.
A yau Talata ake sa ran shugaba Trump zai yi wani jawabi ta talabijin ga al’umar kasar, gabanin ziyarar da zai kai kan iyakar ta Amurka a ranar Alhamis.
A jiya Litinin, mataikamakin shugaban kasa, Mike Pence, ya jaddadawa manema labarai cewa akwai “matsala sahihiya” akan iyakar Amurka, yana mai dora laifin akan ‘yan Democrat, wadanda ya ce sun ki su amince a bude ma’aikatun da aka rufe.
Sai dai shugaban ‘yan Democrat a majalisar Dattawa Sanata Chuck Schummer a wani jawabi da ya yi jiya Litinin, ya ce, idan har suka mika wuya ga bukatar ta shugaba Trump, hakan zai sa a shiga mummunan yanayi.