WASHINGTON, D. C. - Sai dai Isra’ila na fargabar lamarin ba zai dore ba sanadiyyar sabon yakin da ya barke a Gaza.
A wannan watan Turkiyya ta dakatar da duk wata huldar kasuwanci tsakaninta da Isra'ila har sai an kawo karshen yakin sannan kuma a shiga da kayayyakin agaji cikin Gaza ba tare da wata tangarda ba.
Isra'ila ta ce matakin da Turkiyya ta dauka ya saba wa ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya.
Masu shigo da kaya na Isra'ila sun yi ta fadi-tashi don nemo wasu hanyoyin samun wasu muhimman kayayyaki da suka hada da siminti zuwa abinci da motoci a matsayin martani ga matakin da Turkiyya ta dauka, wanda masana tattalin arziki ke ganin zai iya haifar da karancin na karamın lokaci amma da wuya ya durkusar da tattalin arzikin Isra'ila mai karfin dala biliyan 500.
Shmuel Abramzon, babban masanin tattalin arziki a ma'aikatar kudi ta Isra'ila, ya ce, "Turkiyya babbar abokiyar cinikayya ce ta Isra'ila amma ba su dogara da Turkiyya kadai ba," in ji Shmuel Abramzon, babban masanin tattalin arziki a ma'aikatar kudi ta Isra'ila, wanda a yanzu ya yi imanin ci gaban tattalin arzikin Isra'ila na 2024 zai wuce 1.6% a hasashen yanzu.
-Reuters