Kerry yana Istanbul yau Lahadi inda zai gana da Firai Ministan kasar Turkiya Ahmet Davutoglu da Firai Minista Recep Tayyip Erdogan.
A wani taron manema labarai na hadin guiwa da ministan harkokin kasashen ketaren, Kerry ya bayyana cewa, yana da muhimmanci Turkiya da Isra’ila su cimma matsaya dangane da diyyar da za a biya a kan abinda ya kawo rashin jituwa tsakanin kasashen shekaru uku da suka shige, lokacin da ‘yan kasar Turkiya takwas da kuma wani Ba’amurke dan asalin kasar Turkiya suka mutu a wani sumame da Isra’ila ta kai kan ayarin kananan jiragen ruwan Turkiya dake kan hanyarsu zuwa zirin Gaza.
Turkiya da Isra’ila dukansu muhimman abokan kawancen Amurka ne, muna kuma kyautata zaton amincewa da sake daidaita dangantaka tsakanin kasashen zai taimaka wajen bude kofar hulda mai girma.
Dangane kuma da rikicin da ake yi a makwabciya Siriya, Kerry yace, Amurka da Turkiya suna da manufa daya na ganin an mika mulki cikin kwanciyar hankali a Siriya. Yace Turkiya tayi kokari ainun wajen tallafawa ‘yan gudun hijirar kasar Siriya dake cikin kasarta.