Kasuwa: Farmers Market, Abuja

Shirin kasuwa na wannan makon ya sake kai ziyara kasuwar Farmers Market da ke birnin Abuja don jin halin da kasuwar ta ke ciki a 'yan kwanakin nan.

'Yan kasuwar Farmers Market da ke unguwar Maitama a Abuja babban birnin Najeriya sun koka akan rashin ciniki a 'yan kwanakin nan saboda zaman fargaba da ake fuskanta a sassan Najeriya daban-daban, musamman sakamakon zanga-zangar da matasa ke yi ta neman a yi garambawul a bangaren 'yan sandan kasar. Wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar ta tattauna da wasu 'yan kasuwar.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasuwa: Farmers Market, Abuja