Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

#EndSARS: Shugaba Buhari Ya Yi Jawabin Kwantar Da Hankali


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jawabi don kwantar da hankulan ‘yan kasa kan kisan matasa masu zanga-zanga.

Bayan koke-koke daga ‘yan Najeriya da dama, shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa ‘yan kasar jawabi a kan kisan wasu masu zanga-zanga da ake zargin jami’an rundunar soji da aikatawa yana mai rokon yan kasa su rungumi zaman lafiya.

A jawabin sa ga ‘yan Najeriya, shugaba muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya zama wajibi ya yi magana da su bayan korafe-korafe da ya samu daga bangarori daban-daban a kan yanayin da ake ciki a kasar da kuma ganawa da ya yi da manyan hafsoshin tsaro yana mai gargadi ga marasa kishin kasa da ke amfani da damar masu zanga-zangar lumana na #ENDSARS domin cimma manufa na daban su gujewa cigaba da hakan.

Shugaban ya kuma bayyana rashin jin dadi game da rahoton da ya samu a ranar litinin na yin amfani da karfi kan masu zanga-zanga yana mai cewa ‘yan Najeriya na da yancin gudanar da zanga-zanga kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar sashi na 40 ya tanadar ba tare da takewa safran ‘yan kasa yancin gudanar da ayyukan su na yau da kullum ba.

Shugaba Buhari ya bayyana damuwa matuka kan rasa rayyuka da dukiyoyi yana mai jan hankanli kasashe makwabta da sauran kasashen duniya su rinka bincike domin gano gaskiyar lamarin dake faruwa kafin su dauki matakai cikin gaggawa a kai inda ya roki matasa masu zanga-zanga su yi hakuri su rungumi zaman lafiya kuma gwamnati zata aiwatar da dukkan bukatun da suka mika.

Yanzu abun jira a gani shi ne yadda matasa zasu dauki jawabin shugaba Buhari.

Saurari rahoton Halima Abdulra’uf cikin sauti:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jawabi don kwantar da hankulan ‘yan kasa kan kisan matasa masu zanga-zanga - 3' 37"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari



  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG