Kasashen Sahel Da Jamus Sun Tattauna Kan Dalilan Da Ke Haddasa Ta’addanci

Dakarun mali suna atisaye a karkashin horon dakarun Amurka a Timbuktu a ranar 18 ga watan Maris din shekarar 2004, file photo. Malian soldiers

‘Yan majalisar dokoki daga kasashe hudu na yammacin Afirka sun gudanar da taro a karshen makon da ya gabata a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast tare da halartar wasu takwarorinsu na Jamus don tantaunawa akan matsalolin da ke haddasa ayyukan ta’addanci a nafiyar Afirka.

Akalla hare-haren ta’addanci kusan 5000 aka kai cikin shekarar 2015 a wasu sassan nahiyar Afirka a cewar shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin Nijar, Alhaji Hamma Assa.

Shugaban kwamitin ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wakilin Sashen Hausa na Muryar Sule Mumuni Barma a Yamai.

“A ganinmu, wasu suna fakewa a bayan addini wasu kuma suna buya akan harkar sayar da kwaya wasu kuma talauci ya yi masu katutu.” In ji Assa a lokacin da wakilinmu ya tambaye shi dalilan da ke haddasa ayyukan ta’addanci a nahiyar Afirka.

Shugaban kwamitin ya kara da cdewa lallai an ragewa ‘yan ta’addan karfi a yankin kogin tafkin Chadi a ‘yan watannin nan amma ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba.

“Yanzu abinda yake kamari shi ne iyaka da Mali wanda yake ana kawo hari ko da yaushe.” Ya kara da cewa.

Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin matakan da kasashen suka dauka domin kara shawo kan wannan matsala:

Your browser doesn’t support HTML5

Kasashen Sahel Da Jamus Sun Tattauna Kan Dalilan Da Ke Haddasa Ta’addanci - 2'45"