Kungiyoyi masu zaman kansu a Jamhuriyar Nijar, sun kare kansu daga zargin da gwamnati ta yi masu na cewa ba sa ba da rahoton ayyukan da suke gudanarwa na tallafawa mutane a kasar a karshen shekara.
A wani taro da ma’aikatar raya karkara ta shirya a farkon makon nan gwamnatin ta kalubalanci kungiyoyin.
Gwmanatin ta yi ikirarin cewa ta kan ba wasu kungiyoyi masu zaman kansu tallafin kudade da horo domin taimakawa al’umar kasar, amma ba sa fitar da rahoto kan aikace-aikacensu.
Amma kungiyoyin sun yi zargin cewa tallafin gwamnatin ba ya kai wa gare su.
"Na farko babban laifunsu shi ne ba sa kiran dukkan wakilan kungiyoyi ba, wadanda su ka kasance na gaske masu aiki cikin Nijar. Babu wani taimako da gwamnati ta ke yi wa wadannan kungiyoyi masu zaman kansu."
Ya kuma yi zargin cewa wasu kungiyoyin, ma'aikatan ma'aikatar ta raya karkara ne suke kafa ta domin amfanin kansu ba tare da sun yi komai.
Sai dai Sakatare Janar a ofishin ma’aikatar raya karkarar, Alhaji Ibrahim Adamu, ya ce akwai dalilin da ya sa gwamnatin ba ta sakar masu mara.
“Gwamnati ta fitar da makudan kudi aka raba masu aka ce shekara mai zuwa za a sake, amma da shekarar ta kare wadanda suka yi aikinma ba su samar da rahoto ba kan aikin da su ke yi ba.”
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:
Facebook Forum