Gwamnatin tace zata rage musu haraji kuma zata basu tallafin da duk suke bukata domin yin hakan zai samar da aikin yi cikin kasa.
Hajiya Fatima na daya daga cikin ire-iren wadannan mutanen da ta dawo daga kasar Faransa, kuma wakilin Muryar Amurka Awal Garba ya tambaye ta kome ya bata sha’awa ta amsa wannan kiran?
‘’Wato abinda ya bani shaawar dawo gida kasar Cameroon bude kanfanin sarrafa ruwan sha shine domin na taimaka wa ‘yan uwa na na kasar Cameroon, haka ita ma gwamnati ta dafa muna kan wannan kudiri namu, tace daga shekaru biyu zuwa biyar zasu rage muna haraji’’.
Malama Aisha ita ma daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato (Dubai) da niyyar bude maaikatar dinkin hannu, kamar zanin gado da kuma kujerun daki.
‘’Ina son in taimakawa kasa ta nima inga taci gaba kuma gashi ance za ayi muna ragin haraji hakan kuma zai taimakawa matasa su samu aiki’’
Ga Muhamma Awal Garba da Karin bayani.
Facebook Forum