Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Burundi Shida Sun Yi Batan-dabo a Amurka


Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza a ranar 23 ga watan Fabrairu a Bujumbura. (REUTERS/Evrard Ngendakumana)
Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza a ranar 23 ga watan Fabrairu a Bujumbura. (REUTERS/Evrard Ngendakumana)

An nemi wasu matasan kasar Burundi su shida an rasa, yayin da ake gab da kammala wata gasa da ta tattaro dalibai daga sassa daban na duniya zuwa Amurka domin halartar wannan gasa.

Wasu matasa har su shida da suka shiga gasar sarrafa mutum-mutumi a Amurka sun bata, in ji jami'an rundunar ‘yan sandan Washington.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Margarita Mikhaylova, ta ce an ga biyu daga cikin wadannan matasan da suka hada da Audrey Mwamikazi dan shekaru 17 da Don Ingabire 16 suna tsallaka kan iyakar Amurka da Canada.

Su kuma sauran yaran hudu an yi musu ganin karshe ne da hantsin ranar Talata bayan an kammala zagayen farko na gasar.

An dai samar da wannan gasar ne domin ta kara wa matasan hazaka da kuma sha'awar darasin lissafi da na kimiyya.

Kasashe sama da 150 suka kawo matasansu domin shiga wannan gasar kuma ko wane yana da dan rakiyarsa da ya mallaki hankalin sa.

Rundunar ‘yan sandar ta ce ita ba ta da masaniyar inda Nice Munezero, dan shekaru 17,Kevin Sabumukakiza shi ma dan shekaru 17 da kuma Richard Irakoze dan shekaru 18, da Aristide Irambo shimawani dan shekaru 18, kuma bisa ga dukkan alamu ba wani kumbuya-kumbuya cikin lamarin.

Shugaban kamfanin First Global, Kamfanin daya shirya wannan gasar, Joe Sestak shine ya fara kiran ‘ya sanda game da bacewar wadannan yaran su shida, bayan ya samu labarin cewa shugabnan tawagar yaran kasar Burundi bai ji duriyarsu ba.

Yanzu haka dai ana ci gaba da neman su.

Kasar Burundi, wacce ke gabashin Afirka na da yawan jama'a miliyan 10, ta kuma sha fama da rikice-rikice a 'yan shekarun da suka gabata.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human rights Watch ta ce an kashe daruruwan mutane tare da ganawa wasu azaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG