Kasashen Duniya na Cigaba da Muzgunawa 'Yan Najeriya Kan Ebola.

Tsohon wakilin najeriya a zauren majalisar dinin duniya Alhaji Yusuf Maimata Sule Dan Masanin Kano, yace matakan nuna wariya da muzgunawa ga ‘yan najeriya a bisa dalilin cutar Ebola a wasu kasashe ya sabawa dokoki da sharrudan diplomasiyya na majalisar dinkin duniya, tunda hukumar lafiya ta duniya ta fitar da najeriya daga jerin kasashe masu fama da cutar Ebola.

A juma’ar data gabatane aka rawaito ministan harkokin waje na Najeriya Alhaji Aminu Wali na bayyana damuwa kan yadda haryanzu wasu kasashe guda ashirin da biyu ke nuna wariya dama musgunawa ga ‘yan Najeriya a dalilin zargin cutar Ebola duk kuwa da nasarar da Najeriyar tasamu wajen kawar da wannan cuta baki dayanta, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar.

A yayin wata ganawa da jami’an dipplomasiyya na kasashe daban daban acan Abuja, ministan yace abin takaicine yadda kasashen ke bullo wasu manufofi na tsamgwama da musgunawa ga ‘yan Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasashen Duniya na Cigaba da Muzgunawa ‘Yan Najeriya Kan Ebola - 2'50"