Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Zafafa Daukan Matakan Gwajin Cutar Ebola.


Travelers coming from West Africa face Ebola screening at five U.S. airports, starting with New York's JFK International on Oct. 11, 2014.
Travelers coming from West Africa face Ebola screening at five U.S. airports, starting with New York's JFK International on Oct. 11, 2014.

Wani filin jirgin saman birnin New York ya zama na farko a kasar Amurka da ya fara zafafa daukan matakan gwajin cutar Ebola.

Daga yau Asabar babban filin jirgin saman Kennedy na New York ya fara gwajin matafiyan dake zuwa Amurka daga kasashen yammacin Afirka na Guinea da Laberiya da kuma Saliyo masu fama da bala'in cutar Ebola.

Jami'ai za su gwada zafin jikin matafiyan dake shigowa, kuma su yi mu su tambayoyin neman gano wasu alamomi.

A mako mai zuwa za a fara irin wannan gwaji a filayen jiragen saman Newark na jahar New Jersey, da Washington, DC, da Chicago a jahar Illinois da kuma Atlanta a jahar Georgia. Daga cikin fasinjojin dake shigowa nan Amurka daga kasashen Afirkan dake fama da cutar Ebola, fiye da kashi 90% na biyowa ne ta wadannan filayen jiragen sama biyar.

A jiya Jumma'a Hukumar Lafiya ta Duniya WHO/OMS ta ce yawan wadanda cutar ta hallaka ya karu ya wuce mutane 4,000.

Hukumar ta ce an samu mutane 8,400 dake dauke da cutar a kasashe bakwai, kuma mutane 4,033 sun mutu sanadiyar ta.

XS
SM
MD
LG